Uncategorized

kalaman soyayya masu dadi 2022

Minene Soyayya?

Kalmar Soyayya na nufin musayar so da kauna tsakanin mutane guda biyu, ko dai ya kasance tsakanin Mace da Namiji, ko tsakanin maza biyu, ko kuma tsakanin mata biyu.

Ita Soyayya takan canza yanayin mu’amala da kuma salon zamantakewa tsakanin masoya juna, a inda zaka samesu su na masu kyautatawa da kuma tausayin junansu.

Zaka samu su na matukar muradin son kasancewa tare babu gajiyarwa, sannan kuma idan sun rabu zaka samu su na matukar kewar junansu tare da muradin son su sake haduwa.

kalaman soyayya masu dadi 2022

Haka kuma basa gajiya da jin muryoyin junansu, haka kuma idan sun dade basu yi magana ba sai dukkan su su shiga kewa da muradi ko zakuwar don jin muryoyin su.

Zaka ga ko da mutum ma’abocin son Kai ne shi, sannan kuma yana da kyashi da hassada da mutunta, amma dukkan wannan munanan halayen yakan tausasa su a yayin mu’amala da abokin soyayyar sa. To da zarar ka ga irin wannan tarayyar kar ka yi tambayar minene Soyayya, kawai ka ga amsar ka.

 

ya ake furta kalaman soyayya masu dadi?

 

Kamar yadda mu ka sani, soyayya tamkar shuka ce kalaman Soyayya kuma ruwa ne da ake yiwa shukar ban ruwa da ita, wadda muddin aka dade ba a bada ruwan ba to shukar za ta bushe.

A saboda haka muna bukatar sanin yadda za mu furta kalaman Soyayya ga wadanda mu ke so ta yadda kalaman mu ba za su zama kamar tatsuniya ba, sannan kuma za su zama zafafan kalaman soyayya masu dadi da za su iya tsuma zuciyar wanda mu ke kauna.

Dalilin haka kuwa shi ne, muddin mu ka ce za mu cika gishiri ko magi a miya munsan ba za ta shayu ba, to haka su ma kalaman soyayya idan an tsawwala su to ba za su bunkasa Soyayya ba sai dai su kashe ta.

Yadda ake furta kalaman soyayya

Duba da yanayin dabi’u irin na zuciyar mutane, yana da kyau kalaman mu su kasance masu iya yin tasiri ga dukkan zuciyar da ta sauraresu. Saboda haka kalaman da aka saba furta Wa na yau da kullum a duniyar masoya ba za su yi ba, sai dai mu kawo sabbi ko da a suka ce ne.

Misali: Masoyiya abar kaunar idan na rasaki nima zan rasa rayuwata.

Kaga a nan ta tabbatar da batunka ba gaskiya ba ne, amma idan zaka ce mata: Aduk lokacin da ki ke a kusa da ni, nakan ji wani shauki da ke sanya ni farin ciki.

A nan ko ita kanta muddin dai so na gaskiya ta ke maka, tabbas zai kasance tana jin yadda ka ke ji.

Hakan zai san har a zuciyarta ta gaskata batunka har ta ji ta kara kaunar ka. za ku ia tuntubar mu a rariyar shafin mu 

ko kuma ku biyo mu a whatsapp kan wannan lambar

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
× How can we help you?